Ashe bai kamata a ce, ka xan tsaya kaxan ba, don ka samu cikakkiyar masaniya kuma mai zurfin game da addinin da ya fi kowane addini, aka kuma fi yawan karvarsa, kamar yadda qididdigar duniya ta nuna?..Ashe bai kamata a ce, kana jin wani irin daxi ba, a duk lokacin da ka san wani abu game da ilimi, da wayewa, da al’adu, da falsafa da tsarin rayuwar wasu mutane da suke rayuwa tare da mu a wata duniya, da wani addini? Idan haka ne, me zai hana ka xan yi amfani da damar da kake da ita, ka karanta wannan littafi domin ka san tantagaryar abin da addinin Musulunci ya qunsa, na gaskiya, wanda aka cirato daga ingantattun tuwasu da asullansa. Sa’annan ka auna su da lafiyayyen hankali da tatacciyar basirarka. Me zai hana? Ida har amsarka ga gaba xayan waxannan tambayoyi ita ce, eh! to, lalle kuwa domin ka aka wallafa wannan littafin.